Rundanar ‘yan sanda ta kasareshen jihar Kano, ta karyata wata jita jita da ta yadu a jihar Kano kan cewar, za’a kaiwa makarantun boko hari, a dahaka ake cewar iyaye su garzaya domin kwashe yaransu daga makarantun, a cewar sanarwar da ‘yan sanda suka karyata.

Wannan jita jita ta yadu a kafar sadarwa ta zamani da aka fi sani da ‘Social media’, inda aka ce akwai yuwuwar ‘yan ta’adda zasu yi garkuwa da wasu daliban makarantun boko musamman na kwana a jihar Kano, sanarwar da ta haifar da firgici a zukatan iyaye da yawa.

Haka kuma, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano,Magaji Musa majiya, ya karyata wannan jita jita,inda yace wannan ba komai bane sai aikin wasu batagari masu son kawowa al’umma firgici da razani.

Haka kuma, kwamishinan yada labarai da matasa na jihar Kano, Mohammed garba, ya karyata wannanjita jita shima,inda yayi kira ga al’umma da su yi watsi da sanarwa da ba tada inganci, yace, iyaye su kwantar da hankalinsu yaransu na cikin aminci, ya kuma yi kira ga makarantun Gwamnati da su bude domin yin aiki a gobe.

Bayan haka kuma, hukumar da ke kula da makarantun Sakandire ta jihar Kano, ta yi kira da ayi watsi da sanarwar da ta bayar tun da farko inda ta yi kira da a rufe makarantun Gwamnati har sai zuwa wani lokaci, tace Shugabannin makarantu su bude domin yin aiki kamar yadda aka saba.

LEAVE A REPLY