Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta sanar da nasarar da ta samu na kama bindigu 179 da ma’ajiyun alburusai 577 daga hannun jama’a.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Zaki Ahmed ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a birnin Fatakwal a jiya Talata.

Ahmed ya ce daga cikin bindigun da aka kama akwai: AK-47 guda 27 da “Pistol” kirar Nijeriya guda 51 da kirar “Single Barrel” guda 33 da harbi-ka-labe guda 21 da kuma sauran nau’ikan bindigu guda18.

Kwamishinan ya yi wa jama’a tuni akan umurnin da Sufeta Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris, ya bayar na cewa kafin wa’adin kwanaki 21 ya cika, duk wanda ke da haramtaccen makami to ya mika shi ga hukuma.

“Ina kara rokon jama’a da su mika makamansu ga hukuma kafin wa’adin kwanaki 21 ya cika ko kuma a dauki mummunan mataki akan su” inji shi.

Ahmed ya kara da cewa a kullum ‘yan sanda kokari suke yi domin su kiyaye rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

LEAVE A REPLY