‘Yan sanda a jihar Bunuwai sun tabbatar da kame wasu fulani makiyaye 8 sakamakon zarginsu da ake yi da kashe wasu muyum 10 da wasu masu gadi mutum 7 a kauyen Guma dake yankin karamar hukumar Logo ta jihar a ranar litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Moses Yamu ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a ranar Laraba a Mukurdi.

“Makiyaya mutum 8 da 6 a Guma, da kuma mutum biyu a Logo duk sun shiga komar ‘yan sanda sakamakon zargin da ake yi musu na yin kisan gilla ga wasu mutane” Inji Kakakin rundunar.

Ya kara da cewar, rundunar ‘yan sandan jihar, ta tura wata runduna ta musamman a yankin da abin ya faru, domin kare sake aukuwar irin wadannan kisan rashin imani da Fulani makiyaye suke yi.

Mista Yamu, wanda mataimakin sufuritanda ne, ya bayyana cewar yanayin da ake ciki a kananan hukumomi guda biyu, ya sanya rundunar ta mayar da hankali kan yankunan, kuma tuni aka kaddamar da bincike musabbabin wadannan kashe kashe.

Ya kara da cewar “Maharan sun kai farmaki ga kauyen Tomater a yankin Sangev dake karamar hukumar Guma, sannan kuma sun sake kai wasu hare haren a kauyukan Akor da Nzorov da kuma kauyen Bakin Kwata a yankin Umanger duk a karamar hukumar Guma”

“Daga cikin wadan da aka kashe din sun hada da, mutum bakwai daga cikin kungiyar ‘yan sintiri ta jihar Bunuwai, sannan suka bankawa motarsu wuta, kana kuma aka jikkata mutane da dama a tsakanin 31/12/2017 da kuma 02/01/2018.

“Haka kuma, garin Agba-Uko dake kusa da kauyen Azege da kuma Tse-Age duk a yankin karamar hukumar Logo sun fuskanci wadannan hare hare, domin an kashe mutu guda tare da jikkata mutane da dama da kuma cinnawa wani babur wuta”

“Dukkan wadannan da suka samu raunuka, suna kwakkwance cikin asibitoci da dama a fadin jihar suna karbar magani”

Rundunar ‘yan sandan jihar, ta aike da wata tawagar kwararru, wadda mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar ACP Emmanuel Adesina ya jagoranta domin farautar wadannan Fulani makiyaya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, Rahoton da Gwamnatin ta fitar wadda yake tabbatar da dokar hana Fulani makiyaya yin kiwo a yankun ne ya soma aiki tun 1 ga watan Nuwamban shekarar 2017.

Dokar kuma tace, duk wani Bafylatani da aka kama yana kiwo a yankunan za’a daureshi Shekaru biyar ko tarar Naira Miliyan daya.

Wadannan hare hare dai su ne irin su na farko a wadannan yankuna, tun bayan zartar da waccan dokar da Gwamnatin jihar ta yi.

NAN

LEAVE A REPLY