Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandar jihar Kaduna, a jiya Talata, ta cafke wasu mutum biyu da ta ke zargi da kashe dalibin jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

Daliban wanda dan ajin farko a tsangayar kimiyyar likitancin dabbobi, ya gamu da ajalinsa ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Zuwa yanzu dai, ba a gama tantance ko mene ne aihahin musabbabin kisan nasa ba, sai dai, ‘yan sanda na tsaka da bincike don gano yadda lamarin ya faru.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya tabbatar da faruwar kisan a jiya Talata, kuma ya fadawa manema labarai cewa tuni bincike ya yi nisa wajen gano musabbabin kisan kuma har hukumar tasu ta kama mutum biyu da take zargi da hannu a kisan.

Ya ci gaba da cewa, “Mun kama mutum na farko a ranar Lahadi, shi kuma dayan a ranar Litinin, kuma sun amsa tambayoyin ‘yan sanda, abinda ya rage kawai shi ne mu maka su a kotu,” inji Muktar Aliyu.

LEAVE A REPLY