Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wani Fulani makiyayi da bindiga kirar AK-47.

Kakakin rundunar, DSP Ebere Amaraizu shi ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Amaraizu ya ce sun samu nasarar cafke makiyayin ne bayan wani kiran gaggawa da suka samu daga wajen mutanen gari.

Ya ce banda bindigar, sun kuma samu alburusai a hannun makiyayin.

Ya ce makiyayin na cikin wata gona a garin Isigwe-Ugbawka da ke karamar hukumar Nkanu East a lokacin da suka riske shi.

“Ya na taimaka wa ‘yan sanda da bincike,” Amaraizu ya ce game da makiyayin da aka kama.

A karshe ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bawa rundunar ‘yan sandan hadin kai wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya.

LEAVE A REPLY