Ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan

A ranar Litinin din jiya ne ‘yan sanda suka dinga harbahayaki mai sa kwalla a harabar Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, sakamakon dafifi da wadan da suka aiwatar da zaben Shugabannin jam’iyyar a matai na jiha suka yi a harabar Sakatariyar APC ta kasa domin amincewa da su.

An dai samu yamutsi sosai a yayin taron a jiya, inda jihohin da suka gudanar da zaben kashi biyu, duk Shugabannin da suke ikirarin an zabe su suka halarci harabar Sakartariyar jam’iyyar domin uwarjam’iyyar ta kasa ta amince da su a matsayin zababbun Shugabanni.

Lamarin dai ya baci a bakin harabar shiga Sakatariyar jam’iyyar, inda ‘yan sanda tare da wasu zababbun Shugabannin jam’iyyar Na jihohi suka yi ta bata kashi a tsakaninsu, inda aka dinga jefe musu barkonon tsohuwa ko hayaki mai sanya kwalla.

Ministar mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu na daga cikin mutanan da suka tsinci kansu a wannan hali a harabar shiga Sakataraiyar jam’iyyar, inda aka hana su shiga kuma aka dinga harba musu tiyagas babu kakkautawa, duk kuwa da masu tsaronsu sun sanya baki amma abin yaci tura.

 

LEAVE A REPLY