Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yayin da aka harba masa barkonon tsohuwa

‘Yan sanda a jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya sun harbawa Gwamnan jihar Ayodele fayose barkonon tsohuwa, inda ya fadi sumamme nan take.

Rahotanni sun nuna cewar rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tura jami’anta inda suka yiwa gidan Gwamnatin jihar kawanya, suka hana shiga da fita, yayin da Gwamnan jihar Fayose ke cikin gidan Gwamnatin.

An garzaya da Gwamna Fayose zuwa wani asibiti dake cikin gidan Gwamnatin jihar  domin bashi kulawar gaggawa.

Jaridar Daily Nigerian ta habarto cewar, an jiyo karar harbin bindigogi a babban birnin jihar Ado-Ekiti, abinda ya janyo rashin nutsuwa a zukatan al’ummar jihar, musamman wadan da ke cikin babban birnin jihar.

Gwamnan jihar Ayodele Fayose ya tabbatar da faruwar  wannan lamari.

A lokacin da yake sanar da abinda ya faruwa a shafinsa na Twitter Gwamnan yace “Muna jiyo karar harbe harbe a harabar gidan Gwamnatin Ekiti wanda ‘yan sandan da Gwamnatin APC ta tura su mamaye mu suke yi”

 

LEAVE A REPLY