Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sanda  jihar Benuwai ta gurfanar da wasu mutane 28 a gaban kotu kan zargin hada kai wajen kashe wasu Fulani makiyaya guda 10 a jihar.

Fulani makiyayan na cikin fasinjojin da wasu bata gari suka kaiwa hari a ranar Asabar din da ta gabata a kusa da kauyen Yelwata da ke kusa da babbar hanyar Lafia zuwa Markurdi da ke karamar hukumar Guma a jihar.

 Lauyan da ke kare wadanda ake zargi, Mr. Tijani Ahmed, a yayin da ake hira da shi ya tabbatarwa da kafafen yada labarai na gidan talabijin din Channels Television da cewa an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kotun Majistare da ke birnin Makurdi.

Ya yi kira ga ‘yan sanda da su yi kokarin wajen ganin cewa sun kammala bincikensu a kan lamarin domin kotu ta yi sauren yanke hukunci a kan karar da aka mika ma ta.

Kotu a halin yanzu ta daga saurarar karar zuwa 24 ga watan Afrilu.

A yayin da ya ke magana a madadin wadanda suka mika karan, kwamishin rundunar ‘yan sanda jihar Benuwai, Mr. Fatai Owoseni, ya ce an gurfanar da mutane 28 din ne domin ya zama gargadi ga sauran kungiyoyin matasa ko bata gari masu karya doka a jihar.

LEAVE A REPLY