Daga Hassan Y.A. Malik

Rudunar ‘yan sanda reshen jihar Borno ta ce ta dakile wani harin kunar bakin wake da mayakan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa a garin Bama da ke karkashin karamar hukumar Bama a jihar

Mai magana da yawun rundunar, Edet Okon, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a birnin Maiduguri.

Ya ce ‘yan sanda sun kashe ‘yan kunar bakin waken har su 3.

Okon ya ce: “a ranar Litinin 23 ga watan Afrilu da misalin karfe 10:00 na dare wasu ‘yan kunar bakin wake 3 suka yi yunkurin kai hari a yankin Alijari da ke garin Bama kafin su ci karo da ‘yan sanda su.

‘Yan kunar bakin waken a nan take suka tada bama-baman da ke sanye a jikin su, a nan take kowane daga cikinsu ya rasa ransa.

Okon ya ce an aika jami’an sashen ‘yan sanda da ke kula da harkokin da suka shafi bama-bamai domin gudanar da bincike a kan wurin da abun ya faru, bayan binciken na su sun ba al’umma tabbaccin su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mr. Damian Chukwu, ya yi kira ga al’umma jihar da su ci gaba da gudanar da ayyukan su na yau da kullun ba tare da jin tsoro ba.

Kwamishinan ya tabbatarwa al’umma cewa ‘yan sanda za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen ganin cewa sun kare rayukan mutane tare da dukiyoyinsu.

 

LEAVE A REPLY