Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan san jihar Adamawa ta bayyana cewa ta cafke wasu mutum uku a kauyen Tashan-Baba da ke a karamar hukumar Jada bisa zarginsu da hake wata gawa da kuma cirewa gawar kai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Othman Abubakar ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne da kan wata gawa ta yarinya ‘yar shekaru 7 da ba a jima da binnewa ba mai suna Blessing Johnson.
Mutum ukun da aka kama da wannan aika-aiaka sun hada da: Yunusa Audi, Dauda Babale da kuma Mika’ilu Ishaya, kuma tuni suka amsa laifin da aka zarge su da shi na hake kabari tare da datse kan gawa, kuma har sun yi karin bayani da cewa wai wani mutum mai suna John Bakari da ke a kauyen Karhali dake a cikin karamar hukumar Fufore ne ya saka su samo masa kan gawar.

Wadanda a ke zargin sun tabbatarwa da jami’an ‘yan sanda cewa John Bakari ya yi alkawarin biyansu Naira miliyan 5 in suka samo masa kan.

Za a gurfanar da wadannan mutane uku da aka kama a gaban kuliya a yau Litinin.

Tuni dai ‘yan sanda suka ci gaba da farautar John Bakari don shi ma ya gurfana a gaban kotu.

LEAVE A REPLY