Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun cafke wasu maza biyar bisa zarginsu da aikata fyade ga wasu ‘yan mata biyu masu kananan shekaru a yankin Odoside da ke cikin garin Ondo a jihar ta Ondo.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Femi Joseph, ya bayyana cewa wadanda a ke zargi, bayan yin fyade ga ‘yan matan sun azabtar da su sannan suka dauki bidiyon lokacin da suke aikata fyaden akan ‘yan matan suka daura a yanar gizo.

‘Yan sanda sun bayyana sunayen wadanda a ke zargin da: Bode Akinsiku, Olabanji Femi, Abiodun Ayodele, Fadairo Wahab da kuma Adedayo Adebayo.

Wadanda a ke zargin sun daura hoton bidiyon fyaden da suka yi ga ‘yan matan akan shafukansu na Facebook.

‘Yan matan a yayin da suke bayyana yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa, su 4 ne suka ziyarci wadanda a ke zargi sakamakon gayyatarsu da daya daga cikin mazan ya yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ‘yar daya daga cikinsu.

Sai dai biyu daga cikin ‘yan matan sun sha da kyar sakamakon tserwa da suka yi bayan sun fahimci mugun nufin mazan.

Daya daga cikin ‘yan matan, “Sun yi mana tumbir, suka kwace kayanmu, suka kuma shiga yi mana fyade daya bayan daya suna dauka a bidiyo.

“Sun yi barazanar za su kora mu titi ba tare da bamu sutararmu ba, sai da muka yi ta basu hakuri sannan suka barmu muka tafi.

“Tun wajen karfe 11:30 na safe suka tsaremu kafin daga baya su debo mana ruwa mu yi wanka, suka kuma siyo mana shinkafa muka ci kafin su fara lalata da mu.
Bayan sun sallame mu ne muka je muka fadawa wani yayanmu, inda shi kuma ya yi alwashin sai ya samo bidiyon ta yadda zai zame masa shaida a gaban ‘yan sanda.

Kodayake dai wasu daga cikin ‘yan uwan wadanda suka yi mana fyaden sun yi ta rokonmu da kar mu yi karar ‘yan uwansu, har suka yi mana alkawarin bamu kudi a matsayin toshiyar baki, amma dan uwanmu bai amince da tayin ba, inda ya samo bidiyon ya kuma mika shi ga ‘yan sanda don sama mana adalci.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa wadanda a ke zargin za su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata, domin kuwa suna nan suna shirya rahoton gurfanar da su a gaban kotu.

LEAVE A REPLY