Da sanyin safiyar Litinin din nan ne ‘yan sandan kwantarda tarzoma a birnin Maiduguri suka fito domin yin maci kan hakkokinsu da aka gaza biyansu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar ‘yan sanda a birnin na Maiduguri sun yiwa harabar shalkwatar rundunar ‘yan sanda jihar tsinke dake kan titin zuwa Kano a garin na Maiduguri.

Wannan zanga zanga ta ba safai ba dai ta janyo cunkoson ababen hawa a yankin da ake yin zanga zangar, abinda ya jefa razani tsakanin masu ababen hawa kan abinda ka iya faruwa na rashin tsaro a jihar.

Wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewar sun fusata ne akan rashin biyansu hakkokinsu har na tsawon watanni shida.

“A kalla akwai ‘yan sanda guda 10,000 a garin na Maiduguri wanda suke aikin bayar da tsaro sakamakon halin da jihar ta shiga”

“Muna fuskantar tsananin rayuwa saboda rashin biyanmu hakkokinmu, mun kuma nemi a biyamu amma babu wanda ya saurari kokenmu, dan haka muka yanke hukuncin fitowa”

Sai dai kuma a nasa bangaren, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chukwu ya dora alhakin rashin biyan su hakkokinsu akan jinkiri da aka samu na fara aiwatar da kasafin kudin shekarar 2018 da aka yi.

Daga nan ya roki ‘yan sandan su mayar  da wukakensu cikin kube, inda ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba za’a biyasu dukkan hakkokinsu.

LEAVE A REPLY