Dan majalisardattawa, Dino Melaye

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana cewar tana neman dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa ruwa a jallo tare da wani Mohammed Audu dan gidan tsohon Gwamnan jihar Marigayi Abubakar Audu.

‘Yan sandan na neman mutanen biyu ne akn rahotannin karya da suka bayar cewar, ana yiwa rayuwar Dino Melaye barazana a shekarar da ta gabata. haka kuma, rundunar tace, tuni ta aikewa hukumar ‘yan sandan duniya da ake kira Interpol wannan sammaci.

Wannandai ya zo a wata sanarwa da Kwamishinan ‘yaan sanda na jihar Kogi ya fitar Ali Janga, wadda aka aikawa shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa dake Abuja.

Sai dai bayanai sun nuna cewar Sanata Dino Melaye yanzu haka baya Najeriya.

LEAVE A REPLY