Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘ayn sandan jihar Legas sun shiga gudanar da bincike kan yadda wata karuwa mai suna Vivian Bello ta rasa ranta.

An dai samu gawar Vivian ne a cikin bandakin da ke cikin dakin otal din da ta kama a wani Otal mai suna Kings Hotel da ke kan hanyar jirgin kasa da ke tsakanin Ijora zuwa Badia a ranar 13 ga watan Afrilu, 2018.

An kuma sameta da raunika daga kujewa da daujewa da ta yi sakamakon kokawa da aka yi da ita kafin a kasheta.

Shi dai saurayin da ya kawo mata ziyara a wannan dare an neme shi an rasa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Sufurtanda Chike Oti ya bayyana cewa tuni sun tsunduma cikin bincike don gano wanda ya aikata wannan ta’annati.

Ya ce, “Manajan otal din Kings Hotel ya kawo mana rahoton mutuwar wata Vivian Bello da aka samu a mace a daya daga cikin dakunan otal din, kuma an sameta a mace a ban dakin dakin da ta kama kuma dukkan alamu na nuna cewa sai da aka yi gumurzu da ita kafin a yi nasarar kasheta.

“Kes ne na zargin kisan kai kuma muna nan muna bincike akan lamarin don gano yadda abin ya faru.”

LEAVE A REPLY