Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cafke wasu maza biyu masu satar yara, inda daya daga cikin su ke sanye da hijabi.

An kama su ne a ranar 4 ga watan nan bayan da mutanen yankin GRA da ke jihar ta Katsina suka tseguntawa ‘yan sanda zargin ‘yan talikan biyu.

DPO na yankin mai suna CSP Garba Isah ya ce an yi masa korafin cewa an ga wasu maza biyu da ba a yarda da su ba saboda daya daga cikin su na sanye da hijabi, lamarin da ya sa ya hanzarta aikawa da jami’an ‘yan sanda don taho da mutanen.

An samu nasarar kama mazan kuma sun shaidawa ‘yan sandan cewa wani yaro mai shekaru 4 mai suna Muhammad Rabiu suka je sata.

Muhammad Rabiu dai da ne ga mataimakin akannta janar na jihar Katsina, Alhai Rabi’u Gide.

LEAVE A REPLY