Rundunar ‘yan sanda a birni Kano tana tsare da wasu ɗalibai guda 7 da suka fito daga makarantar ‘Gevernment technical College Ungoggo” sakamakon kashe wani abokinsu da suka yi aranar Asabar da daddare.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar kisan ɗalibin tare kuma da tsare ɗaliban da suka kashe shi a ranar litinin dinnan.

Ya bayyana cewar, ɗalibin da aka kashe, Mohammed Ali, yana ajin karshe ne a makarantar Sakandire ta GTC Ungoggo. Shi dai Mohammed, ana zargin abokansa ne suka kashe shi bayan da suka zarge shi da aikata Luwadi.

Majiya yace, daliban sun gayyaci abokin nasu ne wato Mohammed Ali da tsakar daren ranar Asabar, inda suka lakada masa dukan kawo wuka, inda nan take yace ga garin ku nan.

Ya kara da cewar, hudu daga cikin mutum bakwai da ake tsare da su, sun tabbatar da sun kashe Mohammed Ali, a halin da ake ciki, ‘yan sanda na cigaba da gudanar da binciken domin gano yadda aka kashe dalibin.

Tuni dai aka garzaya da gawar Mohammed Ali zuwa asibitin Waziri Gidado dake yankin karamar hukumar Dala a cikin birnin Kano, domin yin gwaje gwajen da zasu tabbatar da sanadiyar mutuwarsa.

LEAVE A REPLY