Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla mutane 115 na ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi na darikar Shi’a ne suka shiga hannun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja bayan da ‘yan shi’a suka shirya tare da gudanar da wata zanga-zangar sai gwamnati ta saki Shaihinsu, Malam Ibrahim El-Zakzaky.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan na Abuja, Anjuguri Manzah, “Ba a yi asarar rai ko daya ba a wajen kokarin hana zanga-zangar, sakamakon kwararru  jami’an ‘yan sanda akan harkar dakile zanga-zanga da rundunar ta aika don dakile zanga-zangar.”

Da fari dai kakakin rundunar ‘yan sandan ta Abuja, Manzah, ya ce ba shi da cikakken bayani game da abinda ke faruwa a wajen da ‘yan shi’ar ke zanga-zangar, sai dai daga baya, a jiya Litinin, Manzah ya bayyyana cewa masu zanga-zangar sun raunata ‘yan sanda 22 tare da lalata motocin ‘yan sanda da wasu kayayyakin gwamnati.

Tun a watan Disambar 2015 ne dai ‘yan shi’a suka fara gabatar da zanga-zanga, bayan da gwamnati ta kama shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta yi kashedi ga ‘yan shi’a da su guji kawo tarnaki ga kawo cikas ga ababen hawa da ke tafiya a kan titina ta hanyar rufe titi da suke yi a yayin zanga-zangar, wanda rundunar ta ce kan jefa mazauna garin na Abuja cikin wani hali.

LEAVE A REPLY