Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta jibge kimanin ‘yan sanda 8,000 a sassan birnin jihar domin musrkushe zanga zangar da kungiyar Kwadago ta kasa ta shirya domin nuna adawa da korar ma’aikata 36,000 daga aikin Gwamnati da Gwamnan jihar Nasir el-Rufai yayi.

‘Yan sanda dauke da makamai ne suke tsaitsaye a dukkan manyan titunan cikin birnin Kaduna, sannan kuma an jibge wasu tarin ‘yan sanda a shalkwatar kungiyar kwadago ta kasa dake titin ‘yanci a Kaduna, da sauran muhimman guraren da ake zaton ‘yan kungiyar zasu bi a yayin wannan zanga zanga.

Rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, suna nan jibge a manyan hanyoyin shigowa cikin garin kaduna wadan da suka hada da hanyar Kaduna-Kachiya, da Kaduna-Zariya da kuma hanyar Kaduna-Abuja.

Mafiya yawancin titunan cikin garin Kaduna sun kasance fayau a wannan safiyar, sabida yadda aka jibge tarin jami’an tsaro a kusan kowace mahadar titi a fadin jihar. Motocin da suke kan tituna dai ba su da yawa, zirga zirga ta tsaya ba kamar yadda aka saba ba.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasaAyuba Wabba na daga cikin wadan da ake sa ran zasu kasance cikin jagororin zanga zangar da sauran ‘yan kungiyar ta kwadago daga ko ina a fadin kasarnan, domin nuna adawa da wannan kora da Gwamnan Kaduna yake yiwa ma’aikata.

Haka kuma, daman tuni rundunar ‘yan sanda da kuma Gwamnatin jihar Kudna suka gargadi masu zanga zangar da cewar kada su kuskura su fito a yau Alhamis, domin kuwa Gwamnati ta hana kowace irin zanga zanga a fadin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya bayyana cewar, kimanin ‘yan sanda 8,000 ne rundunar ta samar domin dakile wannan zanga zanga a jihar domin tabbatar da doka da oda.

“Yan sanda ba zasu nade hannu su zura idanu suna kallon mutane su zo domin kawo damuwa a jihar ba, hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ba zata lamunci duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a ba a jihar”

“Rundunar ‘yana sanda zata yi duk abinda ya dace domin baiwa dukiyar al’umma kariya da tabbatar da cewar wasu bata gari basu zo sun kawo yamusti ko hautsini a jihar ba” A cewar Kakakin rundunar ‘yana sanda ta jihar kaduna Muktar Aliyu.

NAN

LEAVE A REPLY