‘Yan Najeriya da dama sun caccaki Shugaba Muhammadu Buhari kan zuwa Kano da yayi daurin auren ‘yar Gwamnan Kano Fatima Abdullahi Umar Ganduje da dan gidan Gwamnan Oyo Idris Ajimobi da aka yi a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Shafukan sada zumunta na intanet cike suke da kalaman da mutane suka dinga yi kan shugaba Muhammadu Buhari, sabida kin zuwa jihar Yobe da yayi don ya jajantawa iyayan ‘yan matan da aka sace a makarantar Gwamnati dake Dapchi.

A cewar wasu da yawa, Shugaban kasa ya nuna halin ko in kula da ‘yan matan da aka sace suke ciki, bai je jihar Yobe ya jajantawa Gwamnati da iyayan ‘yan matan da aka sace, amma ya kwash jiki ya nufi Kano domin daurin auren ‘yar Gwamna Ganduje.

An daura auren ‘yar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da dan gidan Gwamnan jihar Oyo Ajimobi da aka yi ranar Asabar a fadar mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu. Mutane da yawa ne suka halarci daurin aure ciki har da Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan da jiga jigan jam’iyyar APC.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ya kasance waliyyin yarinya yayinda Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmet Tinubu ya kasance waliyyin ango. An biya sadakin Naira dubu 50,000. Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ne ya daura auren.

LEAVE A REPLY