Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, matsin lambar  ‘yan Najeriya ce ta sanya shi neman wa’adin mulkin karo na biyu a shekarar 2019, wannan bayani ya zo ne daga bakin mai taimakawa Shugaban kasa akan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu.

Shugaba Buhari ya ayyana aniyarsa ta sake neman tarace akan karagar Mulki ne a yayin wani taron sirri na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a sakatariyar  jam’iyyardake babban birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta kara da cewar “Shugaba Muhammadu Buhari a ranar litinin ya yanke shawarar neman tazarce a shekarar 2019”

“Shugaban ya bayyana aniyarsa ta sake neman wa’adin mulki na biyu ne a wani taron sirri na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC”

“Shugaban ya kara da cewar, matsin lambar da yake sha daga ‘yan Najeriya a kullum ce ta sanya shi sake neman mulki karo na biyu (Tazarce) a 2019, yace ya yanke shawarar sanar da majalisar koli ta jam’iyyar a karon farko”

“Kafin dai Shugaban ya bayyana aniyarsa ta sake neman mulki karo na biyu, sai da ya gabatar da wani jawbi gaban wani kwamitin musamman na kwararru da uwar jam’iyyar ta kasa ta kafa”

 

LEAVE A REPLY