Aisha Yesufu

Fitacciyar ‘yar fafutikar ganin an kwato ‘yan matan Chibok da aka sace, Aisha Yesufu a ranar Talata ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tafiyarsa zuwa landan domin a duba lafiyarsa.

Mai magana da yawun Shugaban kasa Malam garba Shehu, a ranar Litinin ya sanar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya ranar Talata domin ya tafi kasar Burtaniya a duba lafiyarsa, kamar yadda likitocinsa suka bayar da umarni.

Da take tofa albarkacin bakinta kan tafiyar da Shugaba Buhari zai yi kasar Burtaniya, Aisha Yesufu ta bayyana cewar, ‘yan Najeriya na bukatar kiwon lafiya na gaskiya domin suma a ceci lafiyarsu.

Aisha Yesufu da take bayyanawa a shafinta na Twitter, tace Shugaba na gari mai kishin jama’arsa, shi ne wanda ya damu da harkar kiwon lafiyarsu, ba ya dinga tafiya kasashen Turai yana barin al’ummarsa a cikin mawuyacin hali ba.

LEAVE A REPLY