A kalla ‘yan majalisar wakilai ta tarayya guda 38 suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai kuma, ana saran mutane 100 daga cikin zauren majalisar wakilai ta tarayya ne ake sa ran suma zasu sauya sheka daga APC zuwa PDP.

An samu yamutsi a zaman majalisar ta wakilai, a yayin da wasu ‘yan majalisar suka dinga ihun nuna goyon bayan jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Chukwuka Onyema.

Kakakin majalisar Yakubu Dogara ya shigo zauren majalisar. inda mambobin majalisar suka dinga ihun “Dogara” “Dogara” “Dogara”.

LEAVE A REPLY