Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar litinin ta ci nasarar ceto wata mata ‘yar Shekaru 48 da ta auka shadda, matar mai suna Aisha Umar, bayan da ta shiga bandaki ne a gidanta, shaddar ta rufta da ita kasa, a ranar Lahadi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwankwana ta jihar Kano, Saidu Mohammed, yace a ranar Litinin wannan abu ya faru a karamar hukumar Gaya a lokacin da matar ta shiga bandaki domin biyan bukatar ta.

Yace, da misalin karfe 6:445 na yamma a ranar lahadi suka samun kiran gaggawa, inda ba tare da bata lokaci ba, suka nufi inda abin ya faru, domin ceto rayuwar matar.

Ya kara da cewar “A lokacin da muka samu wannan kira na gaggawa, bamu yi kasa a guiwa ba wajen tura ma’aikatanmu domin ceto wannan mata, inda cikin mintuna 15 jami’anmu suka isa wannan waje”

Jami’in ya bayyana farincikinsa ganin yadda aka ceto rayuwar wannan mata ba tare da ta ji rauni ko daya ba.

Daga nan ya shawarci jama’a da su zage dantse wajen bayar da agajin gaggawa a duk lokacin da bukatar irin haka ta taso.

LEAVE A REPLY