Hukumar kula da lafiya a matakin farko dake babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda baki ‘yan kasashen waje dake zaune a Abuja suka ki Amincewa da a yiwa yaransu allurar Foliyo a birnin.

Babban Sakataren hukumar, Mathew Ashikeni ya bayyana faruwar hakan a matsayin cin fuska da baki ‘yan kasashen waje suke yi na hana a yiwa yaransu allurar rigakafin kamuwa da cutar Foliyo kamar yadda ake yiwa sauran yara ‘yan Najeriya.

Hukumomin babban birnin tarayya Abuja, sun tsara cewar a kalla yara 619,000 ake sa ran yiwa allurarrigakafin kamuwa dda cutar Foliyo a birnin a wannan watan na Fabrairu.

Mista Ashikeni ya bayyana cewar jami’an da suke yiwa yara allurar ta kamuwa da cutar foliyo, da suka ziyarci unguwar Lautai dake shiyyar Wuse Zone 4 inda galibi baki ‘yan kasashen waje suke zaune, sun dinga kin amincewa da a yiwa yaransu allurar rigakafin kamuwa da cutar ta foliyo.

Haka kuma, Ashikeni ya kara da cewar bakin ‘yan kasashen waje sun yi barazanar matukar jami’an tsaron unguwar suka bari jami’an da suke yin allurar ta foliyo suka shigo cikin yankin nasu to ba zasu biyasu albashin da suke basu na gadin da suke yi musu.

Bayan haka ma, Turkawa ma hana jami’an da suke yin allurar shiga makaraantunsu da inda suke zaune.

A sabida haka ne, Mista Ashikeni yayi roko ga baki ‘yan kasashen waje da su bari a yiwa yaransu wannan allurar domin samun garkuwa daga kamuwa da cututtukan da suke nakasta kananan yara.

LEAVE A REPLY