Hassan Y.A. Malik
 

A yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ne, da misalin karfe 7:35 na yamma, ‘yan fashi da makami a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed, MMA, da ke jihar Legas, suka yi fashi akan jirgin Air Peace kirar Boeing 737 da ke kokarin tashi.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun farmaki jirgin mai lamba 7138 a lokacin da ya fara tafiya a kan titin da zai yunkura ya tashi sama, kuma ‘yan fashin sun bude ma’ajiyar kayayyakin fasinja na jirgin.

Manajan sadarwa na kamfanin Air Peace, ya tabbatar da faruwar wannan labari, haka kuma wata fasinja daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin da aka yi wa fashin, ta bayyana hakan a shafinta na twittter.

A wata samarwa da manajan sadarwa na kamfanin Air Peace din ya fitar, manajan ya ce: “Muna godiya ga daukacin fasinjojin da ke cikin wannan jirgi mai lamba 7138 bisa juriya da hakuri da suka nuna a lokacin da jirgin ya jinkirta bayan wasu sun bude ma’ajiyar kayansa. Muna godiya har lau, ga jami’an kwance bom da suka zo suka tabbatar da cewa wadancan bata gari basu bar wani abu mai fashewa a cikin jirgin ba. Godiya ta musamman ga hukumar filayen jiragen sama ta kasa, FAAN da hukumar tsaro ta FAAN din da sauran wadanda suka taimaka wajen tabbatar da tsaro a lokacin da wasu wadanda muke zargi’yan fashi ne suka bude ma;ajiyar kayan jirginmu a yayin da ya ke shirin tashi, da misalin karfe 7:35 na yammacin Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2018.”

Ko a bara ma sai da aka samu irin wannan a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed, inda bata gari a watab Disambar 2017, suka farmaki wani jirgi da ya sauka daga kasar Turkiya, kuma suka yi awon gaba da jakar daya daga cikin ma’aikatan jirgin.. Sai kuma wani wanda aka yi akan fitattun mawakan Nijeriya, Tiwa Savage da Wizkid a lokacin da suka dawo daga wani wasa da suka je yi a Uyo, jihar Akwa Ibom.

Hukumar jiragen sama ta kasa ta ki bayyana wannan labari.

LEAVE A REPLY