Wasu gungun samari da ake kyautata zaton ‘yan fashi da makami ne a birnin Yenaguwa na jihar Bayelsa sun yiwa wata ‘yar hidimar kasa a jihar fyade su goma sha biyar.

Matasan dai sun yiwa sansanin ‘yan yiwa kasa hidamar ne dake Yenizue Gene a wajen birnin Yenaguwa da misalin karfe 3 na safe a ranar 17 ga watan Yunin nan.

A cewar wata sanarwa ‘yan fashin sun karya lagwon ‘yan kungiyar sintiri dake yankin, inda suka yi ta harbe harbe da bindigogi manya.

 

LEAVE A REPLY