Daga Hassan Y.A. Malik

Mutane 5 sun rasa rayukansu a wani hari da wasu ‘yan daba suka kai a kan garin Bena da ke a karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

Kwamishina ‘yan sandan jihar, Kabiru Ibrahim ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a jiya Talata.

Kwamishina ya ce, ‘yan fashi 11 ne suka kai harin, kuma tuni an cafke su gaba dayansu, inda aka samu mutum 10 daga cikinsu ‘yan asalin jihar Zamfara ne, 1 daga cikinsu kuma dan asalin jihar ta Kebbi.

Ya ce, “‘Yana daban sun kai hari a garin Bena kwanaki biyu kacal bayan sun kai hari akan Koboro, wani kauye da ke iyakar Zamfara da Kebbi.“

“‘Yan daban sun hada da: Lawal Ibrahim, Nasiru Lawali, Yahaya Muhammad, Halliru Shantali, Hussaini Hamisu, Muhammad Nuhu, Habibu Sani, Rilwanu Muhammad, Muhammad Sunusi, Muhammad Bara’u da kuma Abubakar Haruna.”

Kwamishin ‘yan sandan ya kara da cewa tuni dai ‘yan sanda suka kwarara tsaro a bangarorin da ayyukan ‘yan daban ya faru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY