Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumomi a rundunar sojin Nijeriya a jiya Alhamis sun bayyana cewa dakarunsu biyar ne suka rasa rayukansu akan titin Pridang zuwa Bita cikin jihar Borno bayan da motarsu ta taka wata nakiya da aka dasa akan hanyarsu.

Kakakin rundunar sojin, Birgediya Janar Texas Chukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da nufin ya sanar da al’umma ainahin abinda ya faru.

Ya ce, “dakarun rundana ta 271 na sojojin kar-ta-kwana sun gamu da wannan hatsari ne a karamar hukumar Gworza, inda mayakan Boko Haram suka yi musu kwanton-bauna.

“Abin takaici, dakarun soji biyar sun rasa rayukansu a wannan karawa ta hanyar taka nakiya da motar da suke ciki ta yi kuma nakiyar ta tashi da su,” inji Birgediya Chukwu.

Rundunar 271 ta cafke wasu mayakan Boko Haram din tare da tarwatsa wasu da suka arce da bindigunsu da kuma raunika a jikinsu.

Birgediya Chukqu ya kara da cewa rundunar sojin Nijeriya ta ceto mutum tara daga hannun ‘yan Boko Haram a wata fitar aiki da suka yi akan kauyika shida a jihar ta Borno.

Kauyikan da sojojin suka caje sun hada da: Jaje, Anguwan Audu, Major Ali, Dabu Abdullahi, Dabu Wulkaro da Gori Jaji.

Mutanen da sojin suka ceto daga mayakan sun hada da: tsofaffi guda biyu, mata biyu da kananan yara biyar.

Mutanen zuwa yanzu na karbar taimakon likitoci kafin daga baya a damka su a hannun hukumomin da ya dace, inji Birgediya Chukwu.

LEAVE A REPLY