Zanen taswirar Najeriya dake nuna jihar Zamfara cikin jan zane

Akalla mutane 27 ne aka kashe a kauyen Zanuka a yankin karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara a ranar Juma’a.

Binciken DAILY NIGERIAN ya ganao cewar ‘yan bindigar sun karkashe shanu tare da cinnawa gidajen kauyen wuta inda suka kone kurmus.

Tunda farko ‘yan sintiri a kauyen sun tasamma ‘yan bindigar domin dakile kai warin da suka yi nufin yi, amma ‘yan bindigar suka yiwa ‘yan sintirin dake kauyen kofar rago, inda suka karkashe su.

“Mun kirga gawarwakin mutane 27 da aka karkashe” A cewar wani Shugaba a yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Sai dai kuma, da yake zantawa da DAILY NIGERIAN, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu yace a rahoton da yake hannunsu, mutum 15 kacal aka kashe.

Kauyen Zanuka dai na da makwabtaka da kauyen Bawar Daji,inda mahara sunka kashe mutane 60 a wani harin kwanton bauna da suka kai kauyen a watan Maris din da ya gabata.

 

LEAVE A REPLY