Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu sace mutane ne su yi garkuwa da su, sun sace wani Baturen kasar Jamus dake aiki da kamfanin gine gine na Dantata and Sawoa a Kano tare da kashe dan sandan da yake tare da shi har lahira a da ranar yau Litinin.

DAILY NIGERIAN ta habarto cewar kimanin mako guda da ya wuce, wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jar fata dan asalin kasar Siriya a Kano, yayin da suka sace dansa mai shekaru 14, wanda har yanzu ba’a samu labarinsa ba.

Wani da abin ya faru a gaban idonsa, ya bayyana cewar lamarin ya auku ne, da misalin karfe 8 na safe akan titin zuwa Madobi, inda wasu ‘yan bindiga su uku dake tuka bakar karamar mota kirar Golf suka harbe dan sandan dake yiwa baturen rakiya.

“Da farko ‘yan bindigar sun fara harbi a iska ne inda mutanen da ke wajen suka hautsine da guje guje”

“Daga bisani kuma suka harbe dan sandan dake tare da Baturen, wanda yake aikin injinyan gina hanya”

“Haka kuma, harbin kan mai uwa da wabi da maharan suka yi ya samu wasu masu wucewa, inda aka dauke su zuwa asibiti” A cewar Malam Lawan wani da abin ya faru akan idonsa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, ya kuma bayyana cewar sun kaddamar da farautar wadannan mahara.

LEAVE A REPLY