Sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Ibrahim K Idris

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Nassarawa a ranar Talata ta tabbatar da cewar an kashe jami’anta guda uku a kauyen Marabar-Udege dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jiharta Nassarawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Samaila Usman ya shaidawa manema labarai a birnin Lafiya shalkwatar jihar Nassarawa cewar, an yiwa ‘yan sandan uku kisan gilla ne akan hanyarsu ta zuwa kwantar da wata tarzoma da ta taso tsakanin ‘yan kabilarAgatu da Fulani makiyaya.

Ya kara da cewar, tun bayan kisan da aka yiwa ‘yan sanda, rundunar a jihar ta tura wata tawaga ta musamman karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar domin ganin an ciyo kwalar wadan da suka yi wa wadannan ‘yan sanda kisan gilla.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar jihar Nassarawa na makwabtaka da jihar Binuwai wadda ke fama da rikice rikice tsakanin Manoma da Makiyaya.

A saboda haka hasashe na nuna cewar ana iya fuskantar karancin abinci a kasarnan a nan gaba, a saboda wannan rikici da ya shafi inda ake kira da sunan kwanson kayan abincin Najeriya ‘Food baskect of the Nation” matukar ba’a tsayar da wannan rikicin ba.

Haka kuma, Gwamnan jihar Nassarawa, Umar Tanko Almakura ya jajantawa rundunar ‘yan sandan jihara bisa wannan rashi da ta yi na jami’anta.

 

 

LEAVE A REPLY