Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba sun kashe wasu masu aikin gina hanya su hudu a Angwan-Rogo dake Jebu-Miango a yankin karamar hukumar Bassa a jihar Filato kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito.

Wani ganau ya shaidawa NAN cewar, ma’aikatan suna debo yashi ne a yayin da suke aikin lokacin da maharan suka kai musu farmaki.

A lokacin da yake tabbatar da aukuwar wannan al’amari, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev, ya shaidawa NAN cewar gaskiya ne wannan hari ya auku da misalin karfe 11 na safiyar ranar.

“Haka ne, mun samu bayanai na kai wannan hari a kauyen Angwan-Rogo, zamu iya tabbatar muku da cewar lallai mutum hudu sun mutu a sanadiyar wannan hari”

“Mun kuma tabbatar da cewar, mutanan da aka kashe din ma’aikata ne da suke debo yashi a inda suke aiki, kafin aka kai musu hari aka kuma halaka su”

Mista Tyopev ya bayyana sunayen mutanan da aka kashe da Adam Sunday 38 da Jatau Akus 39 da Chonu Awarhai 39 da kuma Marcus Mali dan shekaru  22.

Yace, rundunar ‘yan sandan jihar ta baza jami’an tsaro domin zakulo wadan da suka kai wannan harin. Tuni dai aka kai gawarwakin mutanan zuwa asibitin kwararru na jihar Filato dake Jos babban brinin jihar.

Tuni kuma aka shiga yin bincike ka’in da na’in domin ganin an ganoo tare da hukunta wadan da suka yi wannan aikin ta’addancin.

Daga karshe kakakin ya bukaci al’ummar jihar da su bayar da rahoton duk wani suka ga basu aminta da motsinsa ba a yankunansu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

LEAVE A REPLY