Marigayiya Farfesa halima Idris

Tsohuwar kwamishinar kudi ta jihar Katsina, Farfesa Halima Idris ta gamu da ajalinta a ranar Lahadi yayin da gungun masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Marigayaiya Halima Idris ta fara aikin koyarwa ne a kwalejin Ilimi mai zurfi dake Zariya a shekarar 1983, tun daga wannan lokacin take harkar koyarwa har zuwa lokacin da ta zama Shugabar sashin kimiyya da fasaha na jami’ar Umaru Musa YarAdua dake Katsina a shekarar 2015.

An rantsar  da ita a matsayin kwamishinar Ilimi ta jihar Katsina a watan Nuwambar shekarar 2015.

Wani daga cikin matafiya mai suna Mohammed Sheriff da ya fake daga nisan inda ‘yan fashin suka tare hanya suna jiran karasowar jami’an tsaro domin su fatattaki ‘yan fashin, ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar, tun kusan misalin karfe 6:30 ‘yan fashin suka tare hanya, kuma sun shafe akalla awa daya suna fashi a wajen.

“Daga cikin matafiyan akwai wani jami’in soja da yake tare da ‘yarsa, an bude musu wuta inda suka rasu nan take, yayin da matukin motar tasu ya tsira da munanan raunuka sakamakon harbin da aka yi masa.”

“Haka kuma, sun kashe wani mutum bayan da suka fahimci cewar dan sanda ne, sannan sun kashe mutane da dama, sannan sun yi garkuwa da wasu da yawa a yayin wannan tare hanya da suka yi”

Saidai kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Autin Iwar ya ce ba zai iya tabbatarwa cewa akwai rasa rai ko a’a ba, abinda kawai ya sani shi ne anyi musayar wuta tsakanin ‘yan fashin da kuma jami’an tsaro a daidai kauyen Kateri.

Iyalan marigayiya farfesa Halima Idris sun bayyana cewar za’a yi mata jana’iza a yau bayanSallar Azahar a gidanta dake titin Katuru a layin Sullabawa, a unguwar Sarki a jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY