Daga Hassan Y.A. Malik

Shedikwatar sojin saman Nijeriya ta fitar da sanarwar cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan inda jirginsu mai saukar ungulu ke tashi da sauka na garin Yenagoa, jihar Bayelsa a jiya Lahadi.

Sanarwa ta bayyana cewa jami’an sojin saman da ke bakin aiki a lokacin sun yi nasarar korar maharan bayan da suka dauki lokaci ana dauki ba dadi.

Karawar tsakanin sojin saman da ‘yan bindigan ta yi sanadiyyar rasa ran jami’in sojan sama 1.

Babban hafsan askarawan sojin sama na Nijeriya, Air Mashal Sadique Abubakar ya yi umarni da a gabatar da binciken gaggawa kan faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY