Gwamnan jihar Bayelsa, Serieke Dickson

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba a jihar bayelsa, sun harbe har lahira Ebikimi Okoringa, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Serieke Dickson.

Wani ganau ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar wasu mutane ne da ba’a san ko daga ina suke ba, suka hari gidan mataimaki na musamman ga Gwamnan a yankin karamar hukumar Kolokuma/Opokuma dake jihar ta Bayelsa.

Maharan sun harbe mutumin ne da misalin karfe 10 na dare, bayan da suka bari duhu yayi kuma sahu ya fara daukewa, inda suka yiwa mataimaki ga Gwamnan kwanton bauna a lokacin da yake shirin fita daga gidansa.

Binciken kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya tnuna cewar mutumin da aka kashe, tsohon kansila ne, kuma tsohon Shugaban karamar hukuma, an kuma bashi mukamin mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Bayelsa ba a ma tabbatar masa da hukumar da zai lura da ita ba/

LEAVE A REPLY