Daga Mahmud Isa Yola

Wasu matasa a safiyar yau sun afka wa ofishin kamfanin tsohon sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Babachir David Lawan a Yola.

Matasan wadanda suka yi diran mikiya a gaban ofishin dauke da sanduna da duwatsu sun farfasa gilashin motoci dake harabar ofishin. Ofishin dai ba na siyasa bane, na kamfanin noma na Injiniya Babachir ne mai suna BADAU AGRICULTURAL SERVICES LTD.

Matasan sun aiwatar da hakan ne suna ihun “bama yi, sai Bindow”.

Idan ba’a manta ba dai, lokacin da jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda gwani a jihar Adamawa, tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawan na daga cikin wadanda suka kalubalanci zaben wanda a cewar su, gwamnatin Bindow ta tafka da magudi a zaben.

Cikin wadanda matasan suka farfasa musu motoci yayin da suke cikin ofishin kamfanin akwai tsohon mai bada shawara na musamman a gwamnatin Murtala Nyako Alh Usman Ibrahim, da sakataren kungiyar Kamfen na tsohon dan takarar gwamnan jihar Adamawa Injiniya Markus Gundiri.

LEAVE A REPLY