'Yan PDP a majlisardattawa suna tallafe da Dino Melaye

‘Yan majalisar dattawa daga bangaren adawa sun yiwa Sanata Dino Melaye kyakkyawar tarba yayin da ya sauya sheka zuwa wajen zamansu a majalisar dattawa.

Sanatocin sun mike tsaye domin tarbo Dino zuwa sabon mazauninsa a zauren majalisar ta dattawa.

Dino Melaye dai na shan tataburza da Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello. Ko a makwannin da suka gabata, Dino Melaye ya tsallake siradin yi masa kiranye daga zaman dan majalisar dattawa da aka so yi.

LEAVE A REPLY