Ahmad Babba Kaita da Kabir Babba Kaita

Wasu ‘yan uwa biyu Ahmad Babba Kaita na jam’iyyar APC da dan uwansa Kabir Babba Kaita na jam’iyyar PDP na fafatawa a zaben da ke gudana a halin yanzu na kujerar sanatan yankin arewacin Katsina.

Kabir wan Ahmad ne domin mahaifinsu daya ne.

Ahmad shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya.

Shi kuwa Kabir tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ne wato kwastam.

‘Yan uwan biyu na neman cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.

Duk wanda ya yi nasara a zaben ne zai kasance wakilin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin garin Daura na cikin yankin Katsina ta arewa ne.

BBCHAUSA.COM

LEAVE A REPLY