Yasir Ramadan Gwale

Lamarin dai ya auku ne kamar yadda Yasir Ramadan Gwale ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yayi bayanin yadda wata mai yiwa kasa hidima ta fara gina masallaci a makarantar Sakandire ta Gwamnati dake karamar hukumar Kumbotso, kafin daga bisani Allah yayi mata rasuwa.

Yasir ya bayyana cewar “Jiya wani bawan Allah yake bani wani labari wanda yayi matukar girgizani ainun. Ya bani labarin kamar haka: Wata baiwar Allah ce da aka turo ta jihar Kano domin yin NYSC ko hidimar kasa. Ita wannan baiwar Allah ba Musulma bace, kuma an tura ta babbar makarantar Sakandiren Gwamnati dake garin Kumbotso wato GSS Kumbotso.”

Image may contain: outdoor

“Ita wannan kwafa ko mai hidimar kasa, ta lura duk lokacin Sallah idan yayi, dalibai kan yi Sallah ne a karkashin bishiya ko su samu wani wajen su rabe su yi Sallah. Ganin hakan ko da yaushe, yasa ta nemi hukumar Makarantar ta bata dama domin ta gina masallaci a makarantar, aka bata dama, wannan baiwar Allah ta siyo kayan aiki yashi da bulo da siminti sannan tasa a nemo ma’aikata da zasu dinga yin ginin tana biyansu.”

“Abin mamakin wannan Baiwar Allah gaba daya ginin da take yi babu wani wanda ya tayata ko ya sanya kudinsa a ciki, ita ce kullum take kula da aikin ginin Masallacin, Lokacin da take gina masallacin ta nemi da a samu wani ya aureta domin ya musuluntar da ita, tana yawan nanata batun a aureta a Musuluntar da ita, amma babu wanda ya kula wannan batu nata.”

Image may contain: outdoor

“Kwatsam wannan baiwar Allah bayan da ta koma garinsu domin yin hutu, ta kamu da rashin lafiya, kuma  cikin kankanin lokaci Allah ya yi mata rasuwa. Wannan shi ne labarin da aka bani kan wannan baiwar Allah mai yin hidimar kasa wadda take aikin gina wannan Masallaci.”

“Wayewar garin yau, nace ni kuwa sai naje naga wannan masallaci da makarantar. Nayi sa’a na samu ginin wannan Masallaci yana nan yadda wannan baiwar Allah ta barshi, sannan na kuma zanta da Shugaban makarantar (Principal)  Zakari Kofar Mata, ya tabbatar min da cewar labarin da aka bani dangane da wannan baiwar Allah na gina wannan masallaci haka yake. Ya zagaya da ni cikin ginin masallacin na ganewa idona.”

Image may contain: outdoor

“Hakikanin gaskiya na jima ban ji abinda ya girgizani kamar wannan ba. Ace a garin Musulmi inda Musulmi ne ke yin Sallah, amma wannan baiwar Allah ta dauki wannan gabarar aiki, ba tare da jiran wani ko wasu ba domin sanya nasu kudin a ciki ba. Bugu da kari matar nan ta nemi a aureta a Musuluntar da ita, amma aka rasa wanda zai iya amsa mata wannan bukata. Gashi Allah ya karbi ranta, tana fatan ta zama Musulma. Yanzu sabida Allah mutanan da suke wannan makaranta ba zasu tuhumci kansu kan hakkin wannan baiwar Allah na kin Musuluntar da ita ba? Hasbunallahu Wani’imal Wakeel!”

“Babu wanda zai iya shiga tsakanin Allah da bawansa, Allah yana ganinmu kuma yana duba izuwa zukatanmu, watakila wannan baiwar Allah kafin rasuwarta tayi Imani, Allah shi ne masanin gaibu da abinda ke fake a garemu. Amma saura kadan nayi mata adduar Allah ya kai mata ladan aikinta, amma tunda imaninta bai bayyana a garemu ba zamu kame baki, Allah shi ne yasan abinda ya dace da ita. Ba shakka  wannan al’amari ya girgizani.”

“Abin mamaki wannan al’amari ya faru ‘yan watanni da suka wuce, amma Masallacin yana nan yadda wannan baiwar Allah ta fara ginin, da mutanan wajen, da masu Sallah a wajen, babu wanda yake da tunin cigaba da wannana aikin alheri. Na zagaya ginin na kuma ga yadda wannan baiwar Allah tayi kokari matuka wajen samarda wannan masallaci.”

“Wannan ya sake sauyamin tunani gaskiya. Da yawan aikin alkhairi ba sai kana da tarin dukiya ba, dan abinda kake da shi zaka iya taimakawa komai kankantarsa domin ciyar da addinin Allah gaba. Wannan kuma kalubale ne garemu baki daya, mu zama jakadu nagari ga Musulunci a duk inda muke, lallai Malamai sun gaya mana ba’a sanya wajen baiwa mutum Kalmar shahada.”

“Wanda duk yake fatan cigaba da ginin wannan masallaci yana iya zuwa ya karasa. Masallacin na nan a makarantar Sakandiren Gwamnati dake garin Kumbotso (GSS Kumbotso) dake daura da Al-Mukab City dake da mashiga daga Titin zuwa Zariya kusa da kwanar dawaki. Allah ka bamu iko da zuciyar taimakon addininka.”

LEAVE A REPLY