Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 25 mai suna Dodo Baraje bisa zarginsa da laifin kashe kawunsa da aka bayyana sunansa da Baraje.

‘Ya sandan dibishin din Bangi ne suka cafke Dodo a yayin da ya ke kan hanyarsa ta tserewa.

Wanda ake zargin, wato Dodo, mazaunin kauyen Shirumbu ne da ke karamar hukumar Maraga a jihar Neja, kuma bincike ya nuna cewa Dodo ya kashe kawunsa mai shekaru 50 ne sakamakon wata cacar baki mai zafi da ta shuga tsakaninsu a kokarin mai rasuwan na ya hana Dodo shan burkutun da ya zamar da shan sa al’ada.

Dodo ya tabbatarwa da jaridar Punch cewa ya harbe kawun nasa ne bayan da ya doke shi kawi don ya sha burkutun ‘Suck and Die’.

“Cikin fushi na ruga cikin gida na dauko bindiga na harbe shi, amma ba da nufin na kashe shi ba. Kokarin gyara ni ya ke yi ta yadda zan zama mutum na gari a cikin al’umma wanda ‘yan uwana za su yi alfahari da shi,” Dodo ya ce.

“Ban san mee zan fadawa duniya ba, musamman mai dakina wacce ta ke matukar girmama kawuna. Babu shakka ba a hayyacina na harbeshi ba, ina cikin maye ne.

Kawuna shi ya kula da ni ya dauki dawaniya da rayuwata. Ban taba samun wata matsala da shi ba sai a wannan karin. Ina fata Allah ya yafe min. Na cuci rayuwata,” Dodo ya koka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Muhammad Abubakar ya tabbatar da wannan labari, inda ya yi karin bayani da cewa har sun samu bindiga harbi ka gudu a wajen Dodo.

Kakakin na ‘yan sanda ya kuma ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da Dodo a gaban Kuliya.

LEAVE A REPLY