Daga Hassan Y.A. Malik

A wani rahoto da Jaridar Premium Times ta wallafa, an bayyana yadda da yawan likitocin Nijeriya ke barin kasar domin su yi aiki a wasu kasashe daban.

Wannan lamari dai na haifar da gagarumar koma baya ga fannin kiwon lafiya na kasar.

Wani malami a jami’ar Maiduguri, Shehu Liberty ya rubutawa shugaban kasa Buhari budaddiyar wasika a ranar 31 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki, bayan da ya hadu da wasu likitoci sama da 200 suna neman aikin likitanci a kasar Saudiyya, inda ko a lokacin an dauki mutane sama da 100 aikin.

Likitocin Nijeriya sun dade su na barin kasar zuwa kasashen Amurka, Canada, Saudi Arabia, Birtaniya da sauran su, kamar yadda bincike ya nuna.

Ko a kasar Birtaniya kawai, a watan Yulin 2017, akwai kimanin lokitocin Nijeriya 4,765 da ke aiki.

Bisa wannan dalili ne ya sa Nijeriya ke fuskantar karancin likitoci wanda hakan ba karamin koma baya ya ke haifarwa kiwon lafiya a kasar ba.

Masana sun ce adadin likitocin Nijeriya idan aka kwatanta da adadin mutanen da ke kasar sun yi matukar karanci, inda a yanzu haka akwai ‘yan Nijeriya 3500 ga kowanni likita daya, sabanin mutane 600 da hukumar lafiya ta duniya ta kayyade.

LEAVE A REPLY