Hussaini Maitangaran

Shaidu sun tabbatar da yadda jami’an tsaro farin kaya na SSS suka yi musayar kasurgumin dan ta’addan nan da ya shirya kai harin Masallacin Juma’ah na kofar fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Hussaini Maitangaran da daliban da aka sace a makarantar sakandiren Gwamnati dake Dapchi a jihar Yobe.

Shi dai wannan kasurgumin dan ta’addan Boko Haram yana karbar umarni ne daga sashin kungiyar wanda Al-Barnawi yake jagoranta. A sanadiyar harin da Maitangaran ya kai masallacin Juma’a na cikin garin Kano fiye da mutane 1000 aka bayarda sanarwar rasuwarsu.

DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, a ranar 9 ga watan Satumbar shekarar 2017, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya SSS sun bayarda sanarwar danke mutumin da ya shirya kuma ya kai harin bom din masallacin Juma’an na kofar fadar mai martaba Sarkin Kano.

Amma kuma, a wani bayanai da wata kwararriya akan harkokin inciken da suka shafi tsaro, Ann Mcgregor ta bayyana yadda ake yin kazamar cuwa cuwa tsakanin jami’an tsaron Najeriya da kuma ‘yan kungiyar Boko Haram akankudin fansa da ake karba.

“Tunkusan shekarar2009, aka samu kulla alakar kazamar cuwa cuwar kudade tsakanin ‘yan ta’adda da wasu daga cikin masu shiga tsakani na gida najeriya da kuma na kasashen waje da suke sanya idanu kan kasashen Afurka masu fama da rikici”

“Batun sake ‘yan matan makarantar Dapchi da aka sace, wata makarkashiya ce ta yin kazamin ciniki da samun gwaggwabar riba tsakanin ‘yan ta’addar da kuma wasu daga cikin masu shiga tsakani daga tarayyar Turai da Amurka”

“Haka kuma, masu shiga tsakani kan wannan batu, sun nemi Gwamnatin najeriya ta bayar da makudan kudade da za’a fanso ‘yan matan da aka sace,wadda sashin kungiyar Boko haramkarkashin jagorancin Al-Barnawi ke jagoranta, sannan kuma suka nemi Gwamnati ta saki ‘yan kungiyarda take tsare da su dan ganin ansamu an sako ‘yan matan da aka sace”

“bayan haka kuma, an bayar da labarin cewar, Leah Sheribu ana cigaba da tsare ta sabida ta ki yadda ta bar addininta na kiristanci, wanda wannan batu yafi jan hankalin Gwamnati fiye a komai”

“Akwai kazamar cuwa cuwa da aka tafka kan batun sako ‘yan matan nan tsakanin masu shiga tsakani na Gwamnatain Najeriya da suka kunshi daraktan hukumar tsaro ta farin kaya SSS, Lawal Daura da kuma Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Abdulrahman Dambazau da kuma Ambasada babagan Kingibe wanda shi ne babban jami’i mai lura da harkokin kasashen waje na Najeriya, da kuma Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Malam Abba Kyari a daya bangaren da masu shiga tsakani na ketare dake kasar Suwizalan da ma’aikatan huldar jakandancinsu dake Najeriya”

“Wani kwararren akan harkokin tsaro na kasar Swiss, Pascal holliger da hadin guiwar Mustapha Zanna wani lauya da yake da makaranta mai zaman kanta a Maiduguri wanda yake bayar da ilimikyauta ga yaran da suka rasa iyayansu a sanadiyar wannan rikici na Boko Haram, makarantar dai wata kungiyar kasar Saudiyya ce mai lusa da addinin Musulunci take taimakawa marayu take bayar da kudaden gudanar da ita, Aisha Wakili wata ‘yar Najeriya dake shiga tsakanin Gwamnati da ‘yan Boko Haram ita ce ta wuce gaba wajen ganin an biya ‘yan ta’addar da suka sace ‘yan matan kudin tarayyar turai Euro miliyan 5 da kuma musayar manyan ‘yan kungiyar da suke tsare a hannun Lawal Daura”

“Babbar kasassabar da aka tafka akan wannan batu ita ce ta sakin Husaini Maitangaran, wanda shi ne ya shiryar makarkashiyar kai harin Masallacin Juma’a na kofar fadar Mai Martaba Sarkin Kano, wanda aka kashe akalla mutane 1000,kuma jami’an hukumartsaro ta farin kaya SSS sun cafke shi a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2017. Sakinsa dai na daya daga cikin yarjejeniyoyin da aka kulla kan batun sako ‘yan matan Dapchi” Wannan bayani na kunshe cikin wata Mukala da Ann ta rubuta a ranar 28 ga watan Maris da ya gabata.

A cewar hukumar tsaro ta farin kaya SSS,sannannen dankungiyar Boko Haram sashin al-Barnawi, shi ne ya shirya makarkashiyar kai hare hare da dama a jihar  kano da suka hada da sashin rundunar ‘yan sandan najeriya shiyya ta daya inda mataimakin sifeton ‘yan sanda na kasa yake [zone 1 (AIG)]a ranar 20 ga watan janairun shekarar 2012 da sauran guraren da suka hadar da kasuwar waya ta kano dake unguwar gidan gona duk Maitangaran shi ne ya kitsa kai wadannan hare hare, bayaga harin masallacin juma’ana kofar fadar  Mai Martaba Sarkin Kano dama wasu hare hare da aka kai a jihar Yobe wanda yayi sanadiyar rayuka masu dumbin yawa.

 

LEAVE A REPLY