Gwamnan jhar Kebbi, a lokacin da yake rabawa talakawa kudi kyauta

Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Abubakar Bagudu, a ranar Alhamis da ta gabata, ya rabawa talakawa da manoma  kudade kyauta akan hanya.

Wani ganau ya shaidawa DAILY NIGERIAN a ranar Asabar cewar, Gwamnan yayi ta rabon kudade a lokacin da ya fita rangadin ganin gonakin shinkafa a kauyen Matankari a yankin karamar hukumar mulkin Suru a jihar Kebbi.

Haka kuma, Gwamnan ya shiga cikin kasuwa, inda ya dinga rabawa kananan ‘yan kasuwa kudi.

 

LEAVE A REPLY