Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP ta bayyana jam’iyyar APC mai mulki da cewar kawai tana yaudarar ‘yan Najeriya ne da sunan “Canji” da kuma “Cigaba” wanda a kaikaice cin fuska ne ga ‘yan Najeriya.

Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a babban birnin tarayya Abuja, sanarwarda kakakin jam’iyyar na kasa Kola Ologbondiyan ya fitara ranar Lahadi.

“Ta yaya jam’iyyar APC zata yaudari ‘yan Najeriya da sunan canji, bayan kuma duk kan ‘yan Najeriya sun shaida badakala da kitumurmurar da suka yi a cikin shekaru uku da suka yi akan mulkin Najeriya, har yanzu ‘yan Najeriya ba su shaida wannan canjin na karya da jam’iyyar ta alkawarta ba”

“Mun tabbatar musu da cewar, ‘yan Najeriya ba zasu taba mancewa da alkawuran kanzon kurege da jam’iyyar APC ta yi musu ba, duk a kokarinsu na darewa kan kujerar  mulkin Najeriya, suka cika al’umma da karairayi” A cewar kakakin PDP na kasa.

LEAVE A REPLY