Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Tsohon Sakataren marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, Alhaji Isa_Sanusi_Bayero ya sha da k’yar daga hannun wasu mutane da ba a san su ba, a yayin da suka yi yunk’urin halaka shi, kamar yadda jaridar Daily_Trust ta ruwaito.

Mutanen, wad’anda su biyar ne, an yi zargin cewa ’yan-ina-da-kisa ne da aka d’auki hayar su domin su kashe shi, suka mamaye harabar gidansa da ke Unguwar Sharad’a Kano, inda suka yi ta harba bindigogi a sama da nufin shiga cikin gidan.

Shi dai Isa Sanusi Bayero ya yi aiki da marigayi Sarki Ado ne na tsawon shekara 15 a matsayin Sakatarensa, sai dai a kwanakin baya kuma Sarkin da ke kan karaga a yanzu, Muhammadu Sanusi II ya raba shi da Mukamin sa.

Da yake bayyana yadda al’amarin ya faru, Isa ya ce mutanen su biyar suna d’auke da bindigogi sun isa gidan nasa da misalin k’arfe 7:40 na dare, inda suka rik’a tambayar cewa ina yake.

Isa Sanusi k’wararren matuk’in jirgin sama ne, wanda ya yi aikin tuk’a tsofaffin shugabannin k’asa guda biyar, wad’anda suka had’a da Ibrahim Badamasi Babangida, Cif Olusegun Obasanjo, Abudussalam Abubakar, Sani Abacha da kuma Mista Aled’ Shonekan.

“Ina zaune a falona a lokacin da ’yan bindigar suka zo gidan nawa kuma nan take suka fara harbi a saman iska. Direbana sai ya fita domin ya ga abin da ke faruwa. ’Yan bindigar sai suka nuna shi da bindiga a kansa, suka ce masa ya kai su wurina, inda nake kallon talabijin. Daga bisani sai na bi bayan direban nawa, inda na gan shi tare da d’aya daga cikin mutanen, yana rik’e da bidiga. Ni kuma sai na yi sauri na rufe k’ofa, na koma falo ina kururuwar neman agaji. Dagan an dai sai ’yan bindigar suka gudu ba tare da sun raunata kowa ba,” inji shi.

Kakakin Hukumar ’yan sanda a Jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar al’amarin kuma suna nan sun duk’ufa wajen bincike.

LEAVE A REPLY