Wani yaro dan shekara 13 ya yanke mazakutar wani dan sanda a lokacin da dan sandan ya nemi yin lalata da yaron. Lamarin ya faru ne a yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, lokacin da dan sandan ya gayyaci yaron dan yin lalata da shi.

Dan sandan da aka bayyana sunansa da Insfekta Lawal Mohammed ya kasance kwance cikin jini male-male kafin wani mutum da ba’a gano ko waye ba ya dauke shi ya kaishi wani asibiti dake kusa domin samun kulawar gaggawa.

wata majiya ta bayyana cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na daren Litinin din da ta gabata, a unguwar Tudun Markabu dake yankin karamar hukumar Faskari.

Bayanai sun nuna cewar ko a baya an sha samun dan sandan da laifin yin lalata da kananan yara ta dubura, abinda yayi sanadiyar barinsa daga garin Malumfashi inda aka yi masa sauyin gurin aiki zuwa Faskari.

Daya daga cikin yaran da shi wannan dan sanda yake nema ne ya gaji da abinda dan sandan yake musu, shi ne ya ron ya shirya tare da abokansa, idan sun shiga sun fara yin lalata da dan sanda yaran su banko cikin dakin domin su yi abinda sukai nufin yiwa dan sandan.

A lokacin da majiyarmu ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar wannan lamari. Yace zasu gudanarda bincike da zarar sun samu dan sandan da laifi zasu gurfanar da shi gaban kuliya.

LEAVE A REPLY