Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutum biyu da suka addabi al’ummar garin Sabon Mariga da ke a aramar hukumar Rafi da ke jihar.

‘Yan sanda sun yi nasarar kama mutanen ne bayan da suka samu kiran waya na cewar masu garkuwa da mutanen sun tarfa wasu mutane na garin, inda suke neman a tura musu Naira miliyan 2.5 asusun ajiyarsu na banki ko kuma su tafi da su su yi garkuwa da su.

‘Yan sanda dibishin din Kagara ne suka yi nasarar kama Mohammed Kwairi mai shekaru 23 da Emmanuel Idi mai shekaru 21 a lokacin suna tsaka da aikata laifin.

A cewar daya daga cikin  bata garin da aka kama wato Mohammed Kwairi, ya ce, “Na fada harkar garkuwa da mutane don na samu ‘yan kudaden da zan yi hidimar Sallah da su.

“Na shiga matsi ne kuma ga shi ina da bukatar kudi da zan yi siyayyan abubuwan Sallah. Ban taba tunanin ‘yan sanda za su kama ni ba.

“Yanzu ga shi iyayena sun yi fushi da ni, sun ki su kawo  in ziyara nan inda na ke a hannun ‘yan sanda. Na tabbata sun yi fuyi fushi da ni matuka. Ina fata za su yafe min,” inji Kwairi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa da zarar ‘yan sanda sun kammala bincikensu za su tasa keyar matasan biyu zuwa gaban kuliya don su girbi abinda suka noma.

LEAVE A REPLY