Gwamnana jihar Ribas, Nyesome Wike

Gwamnan Nyesome WIke na jihar Ribas ya bukaci Gwamnati da ta aiwatar da sauyi a dokar nan da aka yi kan masu garkuwa da mutane, inda ya bukaci a dinga yankewa duk wanda aka samu da laifi sukuncin kisa, haka nan suma matsafa da muggan ‘yan fashi da makami.

Gwamnan Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Manema labarai a birnin Fatakwal biyo bayan kisan wani dan ta’adda da jami’an tsaro suka yi a jihar mai suna Johnson Igwedibia wanda aka fi sani da Don Waneey.

Yace ya kamata Gwamnatin tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi su yi aiki tukuru domin ganin an yiwa dokar nan garambawul inda za’a dinga zartarwa da duk wanda aka samu hukuncin kisa ba tare da wani zabi ba.

“Gwamnatin jihar Ribas ta taimakawa da jami’an tsaro da dukkan kayan aiki domin tabbatar da cewar ba’a bar wasu tsiraru sun kawo rashin zaman lafiya a jihar ba, tare da baiwa rayuwa da kuma dukiyar al’umma kulawa”

“A matsayinmu na Gwamnati, zamu tabbatar da cewar babu wani mahaluki da zamu bari yazo haka siddan ya tayarwa da al’umma hankali, ko ya nemi lalata musu dukiyoyi”

“Gwamnati ba zata zurawa mabarnata ido ba, a sabida haka ake tabbatarwa da al’umma cewar, a shirye Gwamnati take ta baiwa rayuwarsu kulawa da kuma dukiyoyinsu, tare da baiwa jami’an tsaro dukkan irin kulawar da suke bukata”

“A sabida haka, mu a jihar Ribas zamu tabbatar an yiwa wannan doka ta masu garkuwa da mutane garambawul, inda zamu bukaci a zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata irin wannan mugun aiki” Inji Gwamna WIke.

Haka nan kuma, Mista Wike ya baiwa jami’an tsaron jihar da su tabbatar sun kamo fitattun ‘yan ta’addar nan da suka addabi jihar su 32 wanda ba’a bayyana sunayensu ba, domin tabbatar da cewar an hukunta su.

Daga nan, Gwamnan ya godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa turo da wata tawaga da yayi karkashin jagorancin Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau zuwa jihar Ribas domin duba halin tsaron da jihar take ciki, tare da taya al’ummar jihar alhinin abinda ya faru na kashe kashen da miyagun mutane suke yi babu gaira babu dalili.

Sannan kuma, Gwamnan ya yabawa rundunar sojan Najeriya a bisa irin yadda take yin kokarin ganin ta magance dukkan wasu ayyuka na ‘yan ta’adda tare da godewa hukumar tsaron farin kaya ta SSS musamman aikin da suka yi na kashe dan ta’adda Don Waney wanda ya dami kowa a jihar.

NAN

LEAVE A REPLY