Daga Hassan Y.A Malik
 

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Manu Yakubu a gaban Kuliya, a jihar Nassarawa, jiya Talata.

Ana tuhumar Yakubu ne da jefa ‘yar shi mai shekaru 6 a rijiya a bisa zargin ta da maita da janyo masa rashin sa’a a rayuwar shi.

Mutumin wanda ke zaune a yankin Gidigidi da ke jahar ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disambar 2017, kamar yadda dan sanda mai kara, James Anata ya bayyana a kotu.

Wani shaida mai suna Samuel Kuje ya fadawa kotun yadda ya samu yarinyar a cikin rijiya a gonar shi a safiyar ranar da abun ya faru. Ya ce da farko ya zaci fatalwa ce, amma bayan ya tambaya ta ce masa sunan ta Jennifer Ayuba.

Ya ce daga nan ne ya je ya kirawo mutane aka fito daga ita daga rijiyar tare da kiran ‘yan sandan da suka kama mahaifin.

Dan sanda mai kara ya fadawa kotun cewa tuni Yakubu ya amsa laifin shi, inda ya shaidawa ‘yan sanda cewa yarinyar da bakin ta ta fada masa ita mayya ce kuma tuni ta kai shi da matar shi gurin ‘yan uwanta mayu saboda a kashe su a wannan shekara.

Ya ci gaba da cewa, Yakubu ya fada masu cewa ‘yar ta shi ita ta kashe kawunta Diour Yakubu da kannenta biyu da suka mutu jim kadan bayan an haife su, kuma ita ta fadi haka da bakin ta.

Yakubu ya ce ya yarda da abubuwan da yarinyar ta fada ne saboda yadda ta ke bata a jeji kuma ba za ta dawo gida ba sai bayan mako daya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Rose Fuji ta daga sauraren karar zuwa ranar 23 ga watan Afrilun 2018.

LEAVE A REPLY