Hassan Y.A. Malik

Takaicin rashin biyan kudin haya da mazauna gidansa basa yi akan kari, ya sanya wani mutum cinnawa gidan nasa wuta da hannunsa har sai da gidan ya kone kurmus.

Mutumin mai suna Idemudia Obamwonyi dai ya gaji gidan ne daga wajen mahaifinsa.

Banda cikin gidan, shagunan da ke kofar gidan guda 20 su ma sun kone kurmus.

Wannan lamari ya faru ne Benin, babban birnin jihar Edo.

Rahotanni sun bayyana yadda Idumodia ya hana jama’a kashe gobarar da ya tayar, inda ya dinga fada masu cewa su bar gidan ya kone tunda gidan baya amfana masa komai sai ma hada shi rigima da ‘yan hayar.

A lokacin da ya tada gobarar, yawancin masu shagunan kofar gidan sun kulle sun tafi gidajensu, hakn ya sanya wasu daga cikin masu hayar suka tafka asara.

Daya daga cikin masu shagunan, Cynthia Obaseki ta ce kayan ta da ya kone a cikin shagon ya kai na Naira miliyan 5.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Chidi Nwanbuzo ya ce su na kan bincike game da lamarin.

 

LEAVE A REPLY